{"id":11288,"date":"2026-06-02T12:46:32","date_gmt":"2026-06-02T12:46:32","guid":{"rendered":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/?post_type=product&#038;p=11288"},"modified":"2026-06-02T12:46:32","modified_gmt":"2026-06-02T12:46:32","slug":"diwanin-wa%c6%99o%c6%99in-aminu-ladan-abubakar-ala","status":"publish","type":"product","link":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/product\/diwanin-wa%c6%99o%c6%99in-aminu-ladan-abubakar-ala\/","title":{"rendered":"Diwanin Wa\u0199o\u0199in Aminu Ladan Abubakar ALA"},"content":{"rendered":"<p>Martaba da \u0199imar mutum su ne suke bayyana wane ne shi a cikin al\u2019umma. Martaba ita ke \u0199unshe wasu sifofi da suka danganci halayya da tunani da \u0199awazuci da zamantakewa a rayuwar mutum. Hasali ma, batun \u0199ima da martabar mutum sun wuce yadda ake ganin su a zahiri. Wato siffofin da suke tattare a cikin \u0199ima da martaba, su ne suke kammala cikar mutum.<\/p>\n<p>Na farko daga cikin wa\u0257annan siffofi shi ne sau\u0199in kai. Mutumin da ya zama mai sau\u0199in kai, ba shi da wuyar mu\u2019amala da sauran jama\u2019a. Sai dai kuma sau nawa ka ta\u0253a cin karo da irin wannan mutum? Mutum ne mai \u0199ana\u2019a da sanin yakamata. Hasali ma, shi mutum ne wanda ba shi da saurin fushi ko kasala, kuma murmushi ko fara\u2019arsa na inganta yanayi cikin hul\u0257a.<br \/>\nIrin wannan mutum yana bayar da goyon baya tare da \u0199arfafa guiwa a rayuwar al\u2019umma. A kowane lokaci \u0199ofofinsa a bu\u0257e suke, wato a shirye yake domin sauraron jama\u2019a da kuma ba su shawara ta gari, kuma duk inda ya je ba ya \u0253uya.<\/p>\n<p>Saboda haka ya kasance aboki ta yadda mutane za su tunkare shi domin ba da shawara dangane da al\u2019amuransu na rayuwa, musamman ma da yake ba batu ba ne na ku\u0257i, face kyawun hali. Shin ko halayenmu suna taimakawa wajen yin mu\u2019amala da zuciya \u0257aya, kuma ko hakan na sa a sami sakamako cikin al\u2019amuran yau da kullum na abokan hul\u0257a? Ba shakka duk wanda ya tafiyar da rayuwarsa a cikin sau\u0199i, to za a ga yadda jama\u2019a suke kewaye shi cikin aminci da ri\u0199on amana.<\/p>\n<p>Wata siffar kuma ita ce ta \u0199arfin hali. A nan \u0199arfin hali da muke magana shi ne na \u0257a\u2019a da ladabi da biyayya. A zubi da tsarin rayuwa, babu abin da ya dace kuma muke bu\u0199ata face \u0199arfin hali domin fa\u0257in gaskiya. Muna kuma bu\u0199atar \u0199arfin hali musamman a lokacin da muka sami kanmu cikin yanayi na yin za\u0253i tsakanin abu mai kyau da kuma marar kyau, a lokacin da babu mai kallon mu.<\/p>\n<p>Muna bu\u0199atar \u0199arfin hali domin kasancewa masu gaskiya da adalci cikin mu\u2019amala da sauran jama\u2019a. da zarar al\u2019umma ta samu mutum mai \u0199arfin hali a matsayin jagora to rayuwar wannan al\u2019umma za ta kasance cikin dacewa. Irin wannan \u0199arfin hali shi ne \u0199ololuwar zama namiji. Akwai kuma ladabi da biyayya cikin aiki ko wajabci. Muna iya tantancewa tsakanin mutum mai \u0199wazo da kuma biyayya. A yayin da imani yake mi\u0199a wuya ga aiki ko umurni, \u0199wazo kuwa himmatuwa ce ga abin da aka sa a gaba.<\/p>\n<p>Su wa\u0257annan siffofi guda uku, idan suka samu a lokaci guda, to ba shakka an yi tanadin abin \u0199warai ga mutum. Wa\u0257annan abubuwa su ne jagora wajen tafiyar da rayuwa. Wato \u0199wazo da mi\u0199a wuya su ne sirrin gina kai, kuma cikin \u0199wazo ne ake gina mutum. Akwai kuma tausayi. Da yawa mukan sami kanmu cikin so da \u0199aunar mutane masu tausayawa. Babu wata hanya ta samun jin da\u0257i tamkar nuna halin tausayawa. Wato farin ciki yana samuwa nan take amma ba ya \u0257orewa.<\/p>\n<p>Jin da\u0257i ko wani abu ne da ke cikin zuciya. Da yawa manzon rahama yakan hore mu da mu bayar maimakon kar\u0253a, musamman ma da yake hannun bayarwa ya fi hannun kar\u0253a. Ba shakka duniya na alfahari da masu tausayi, domin ba a samun nasara sai a cikin tausayawa. Hasali ma ai masu tausayawar nan su ne masu arzi\u0199i a duniya da lahira, kuma da yake sun shayar da al\u2019umma baiwa ta tausayawa, to zukatansu na cike da annuri.<\/p>\n<p>Gaskiya ne cewa fuska ita ce riga, wato ana bu\u0199atar cikakkiyar shiga ta kamala a kowane lokaci. Da ma dai son tufafi cikin ado ba sabon abu ba ne ga tsarin mawa\u0199a. Hasali ma, ai ma\u2019abuta amfani da tufafi na \u0199warai kan ce jikin da aka kyautata shi yakan tafi tare da halayya, sannan daga baya a samu tasiri ga mutum gaba \u0257aya. Wato mutumin da ya sanya tufafi masu kyau yana \u0257auke da \u0199ima cikin daraja ta musamman. Da haka irin wa\u0257annan mutane kan \u0199ara wa kansu himma da \u0199wazo na aiki da armashi, kuma a da\u0257e ana tunawa da su a cikin al\u2019umma saboda irin ayyukan alherin da aka san su da su.<\/p>\n<p>A insaniya irin ta \u0257an adam, abin da ya gabata yanayi ne da ya dace da Aminu Ladan Abubakar (ALAN Wa\u0199a): Wato shahararren mawa\u0199in da muke gabatar da tarihin rayuwarsa da wa\u0199o\u0199insa a cikin wannan littafi mai suna DIWANIN WA\u0198O\u0198IN AMINU LADAN ABUBAKAR (ALAN WA\u0198A). Domin samun cikakken bayanin rayuwa da wa\u0199o\u0199in ALA, mun kasa littafin zuwa babi-babi har guda goma sha uku (13).<\/p>\n<p>Bayan gabatarwa, a babi na farko an yi bayanin haihuwar Alan wa\u0199a, wato mahaifa da kakanni da \u2018yan uwa. Akwai kuma batun aure da iyalansa da iliminsa (karatunsa) da kuma uwa-uba gwagwarmayar rayuwa. Babi na biyu kuma bayani ne a kan matsayin Alan wa\u0199a a duniyar wa\u0199a. Wato lokaci da dalilin fara wa\u0199a da batun uban gida da muradi da fargaba da wasiya da kuma \u0257aukakar ALA a duniyar wa\u0199a.<\/p>\n<p>Daga nan kuma sai batun jigogin wa\u0199o\u0199in Aminu ALA, wato da yake jigogin na da yawa, babi na uku yana \u0257auke ne da wa\u0199o\u0199i na fa\u0257akarwa. A babi na hu\u0257u kuma, mun kawo wa\u0199o\u0199in Aminu Alan Abubakar (ALAN Wa\u0199a) ne masu jigon siyasa.<br \/>\nBabi na biyar kuwa shi ne ya tattaro wa\u0199o\u0199in ALAN wa\u0199a, masu jigon soyayya. A nan \u0257in ma dai ma\u0199asudin samar da wa\u0257annan wa\u0199o\u0199i shi ne so da \u0199auna duka a cikin soyayya. Daga nan kuma sai batun shugabanci (ko jagoranci), wato tsari na sarauta, wadda idan ta tunkaro to dole a kauce. Babi na shida ne yake \u0257auke da wa\u0199o\u0199in ALA masu jigon sarauta. A babi na bakwai kuma, wa\u0199o\u0199in ALA ne masu jigon yabo da kuma jinjina.<\/p>\n<p>Sai kuma babi na takwas, inda a nan mun kawo wa\u0199o\u0199in Aminu ALA ne masu jigo na ganin dama. Wani jigo kuma da yake da ala\u0199a da na wa\u0199o\u0199in ganin dama shi ne na wa\u0199o\u0199i masu jigon talla, a babi na tara. Daga nan kuma sai babi na goma, wanda yake \u0257auke da wa\u0199o\u0199i masu jigon zagin kasuwa. A nan ne msu hikimar magana suke cewa koya ya yi zagi a kasuwa ya san da wanda yake.<\/p>\n<p>A babi na sha \u0257aya, mun kawo wa\u0199o\u0199in ALA ne masu jigon aure, wato batun nan na farko cikin matakan rayuwa. Daga nan kuma sai babi na sha biyu, wato na wa\u0199o\u0199i masu jigon ta\u2019aziya. A babi na sha uku kuma, wa\u0199o\u0199in Aminu ALA ne masu jigon \u0257aukaka. A nan ne muka bijoro da wa\u0199o\u0199in tarihi da rukunin gwagwarmaya da na shahara da na \u0199alubale da kuma uwa-uba na rukunin nasara.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A cikin Diwanin Wa\u0199o\u0199in Aminu Ladan Abubakar (ALA) an kawo tarihin sha&#8217;irin tare da jerin wa\u0199o\u0199insa. An raba wa\u0199o\u0199in zuwa ruwa rukuni-rukuni ta la&#8217;akari da jigoginsu. Sun ha\u0257a da wa\u0199o\u0199in sarauta da na siyasa da na fa\u0257akarwa da na soyayya da sauransu.<\/p>\n","protected":false},"featured_media":11290,"comment_status":"open","ping_status":"closed","template":"","meta":[],"product_cat":[15],"product_tag":[225,224,222,223,226],"class_list":["post-11288","product","type-product","status-publish","has-post-thumbnail","product_brand-alada-adabi","product_cat-noma","product_tag-alan-waa","product_tag-aminu-ladan-abubakar","product_tag-diwani","product_tag-waoi","product_tag-waoin-zamani","first","instock","sale","downloadable","shipping-taxable","purchasable","product-type-simple"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product\/11288","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product"}],"about":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/types\/product"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=11288"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/media\/11290"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=11288"}],"wp:term":[{"taxonomy":"product_cat","embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product_cat?post=11288"},{"taxonomy":"product_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product_tag?post=11288"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}