{"id":11265,"date":"2026-06-02T12:24:42","date_gmt":"2026-06-02T12:24:42","guid":{"rendered":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/?post_type=product&#038;p=11265"},"modified":"2026-06-02T12:27:17","modified_gmt":"2026-06-02T12:27:17","slug":"wasanni-a-kasar-hausa","status":"publish","type":"product","link":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/product\/wasanni-a-kasar-hausa\/","title":{"rendered":"Wasanni A \u0198asar Hausa"},"content":{"rendered":"<p>Ha\u0199i\u0199a wasanni sun kasance wani \u0253angare na rayuwar \u0257an Adam. Wannan kuwa bai tsaya ga kan Hausawa ba kawai, ya shafi dukkanin al\u2019ummun duniya da ke \u0199asashe daban-daban. Sai dai akan sami bambance-bambancen salo da siga na wa\u0257annan wasanni, wanda hakan ya danganta ga al\u2019ada da yanayin wurin zama na masu wannan wasa. Kai! Ba ma \u2018yan Adam ba ka\u0257ai, akwai halittu da dama da ke wasanni iri-iri a tsakanin junansu. Sun ha\u0257a da birrai da karnuka da shanu da ma wasu dabbobin na daban. Baya ga haka, akan samu wasa tsakanin jinsin halittu mabambanta. A irin haka ne ma akan samu \u0257an Adam na wasa da dabbobi irin su karnuka ko birrai ko dawaki da dai sauransu.<\/p>\n<p>Salailan wasannin da Hausawa suka gada tun iyaye da kakanni na fuskantar dusashewa, tamkar dai sauran al\u2019adun Hausawan. Wannan na faruwa ne sakamakon dalilai masu dama wa\u0257anda za a iya ta\u0199aita su da furucin Tasirin zamani. Lura da wannan \u0199o\u0199arin \u0253acewa da mafi yawan wasannin Gargajiya ke yi, akwai bu\u0199atar killace su wuri guda a matsayin wani kundin da zai kasance abin waiwaita a kodayaushe. Yin hakan zai sanya ko da wasannin sun gushe a zamani, za su kasance a killace har Mahadi.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Wannan Littafi ya yi nasarar tattaro nau\u2019ukan wasannin gargajiya har guda \u0257ari biyu da goma sha hu\u0257u (214). An raba aikin zuwa babuka har guda tara. Babi na farko ya kasance shimfi\u0257a ga aikin. A ciki ne kuma aka kawo amfanin wasannin gargajiya. Daga ciki akwai: horo da gyaran hali, da koyar da jarumta, da koyar da hikima da dabara, da motsa jiki da dai makamantansu.<\/p>\n<p>Babi na biyu ya waiwaici tsarin rayuwar Hausawa a jiya da kuma yau. Wannan ya ha\u0257a da addininsu da kuma tsarin zamantakewa da auratayya. Hakan ya kasance \u0199arin haske game da al\u2019ummar da aka yi rubutun kansu. Wato dai tamkar fitila ce ta haska al\u2019ummun da ake magana kansu domin a ji da\u0257in \u0257aukar hoton zuci yayin da ake bayanin ire-iren wasanninsu.<br \/>\nA cikin babi na uku, an yi \u0199o\u0199arin kawo nau\u2019ukan wasannin gargajiyan Bahaushe. An yi hakan ne ta hanyar la\u2019akari da al\u0199alumma daban-daban wurin raba wasannin. Wa\u0257annan matakai sun ha\u0257a da yanayin gudanar da wasannin, da lokacin gudanar da su, da masu gudanar da su da dai makamantansu. A \u0199ar\u0199ashin kowane rukuni an kawo ta\u0199aitaccen bayani mai gamsarwa tare da misalai domin \u0199arin haske.<\/p>\n<p>Kamar dai yadda aka nuna a baya, zamani ya yi tasiri sannan yana ci gaba da yin tasiri kan wasannin gargajiya. Babi na hu\u0257u ya waiwaici irin tasirin da zamanin ya yi kan wasannin. A cikin babin an nazarci dalilan da suka haifar da dusashewar wasannin gargajiyar Bahaushe. Sun ha\u0257a da samuwar ilimin addini da na boko da samuwar yanar gizo da kafafen sadarwa na yanar gizo da dai sauransu. Sannan babin ya dubi irin sauye-sauye da aka samu ga wasu wasannin gargajiyar ta fuskar yadda ake gudanar da su. Daga \u0199arshe kuma sai babin ya nazarci wasu sabbin wasannin gargajiya da Bahaushe ya tsinta a sakamakon Tasirin zamani a kan al\u2019adunsa.<\/p>\n<p>Daga babi na biyar kuwa, har zuwa na takwas, an kawo jerin wasanni ne tare da bayanin yadda ake gudanar da su. Babi na biyar na \u0257auke da wasannin yara maza guda sittin da biyar (65) tare da bayanin kowanne. Babi na shida kuwa wasannin yara mata ya \u0199unsa, guda \u0257ari da uku (103). Babi na bakwai kuwa ya \u0199unshi wasanni ne na tarayya tsakanin yara maza da mata. Adadinsu ya kai talatin da shida (36). Sai kuma babi na takwas da ya \u0199unshi wasannin manya, wa\u0257anda adadinsu ya kasance bakwai (7) kacal.<\/p>\n<p>Babi na \u0199arshe kuwa, wato na tara, yana \u0199unshe ne da jawaban kammalawa. Bayan an kawo jerin manazarta, sai kuma aka biyo baya da ratayen wa\u0257annan wasannin Gargajiya guda \u0257ari biyu da goma sha hu\u0257u (214) cikin tsararran jadawali. An yi hakan ne domin samar da haske ga mai karatu ko bincike, yadda zai samu bayanai masu muhimmanci kan kowane wasa kai tsaye. Ga kowane wasa, an bayyana abubuwa da suka ha\u0257a da:<br \/>\ni. Sunan wasa<br \/>\nii. Masu wasa<br \/>\niii. Rukunin wasa<br \/>\niv. Kayan aiki<br \/>\nv. Amfanin wasa<br \/>\nvi. Sakamakon wasa (Sakamako mai kyau yayin da aka yi abin \u0199warai, ko kuma mummunan sakamako yayin da aka ci karo da \u0199a\u2019idojin wasa)<\/p>\n","protected":false},"featured_media":11266,"comment_status":"open","ping_status":"closed","template":"","meta":[],"product_cat":[15],"product_tag":[217,219,220,218,221],"class_list":["post-11265","product","type-product","status-publish","has-post-thumbnail","product_brand-alada-adabi","product_cat-noma","product_tag-alada","product_tag-gaa","product_tag-tashe","product_tag-wasanni","product_tag-wasannin-gargajiya","first","instock","sale","downloadable","shipping-taxable","purchasable","product-type-simple"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product\/11265","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product"}],"about":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/types\/product"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=11265"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/media\/11266"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=11265"}],"wp:term":[{"taxonomy":"product_cat","embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product_cat?post=11265"},{"taxonomy":"product_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product_tag?post=11265"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}