{"id":11261,"date":"2026-03-16T23:10:23","date_gmt":"2026-03-16T23:10:23","guid":{"rendered":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/?post_type=product&#038;p=11261"},"modified":"2026-03-16T23:10:23","modified_gmt":"2026-03-16T23:10:23","slug":"wa%c6%99o%c6%99in-hausa-na-gargajiya","status":"publish","type":"product","link":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/product\/wa%c6%99o%c6%99in-hausa-na-gargajiya\/","title":{"rendered":"Wa\u0199o\u0199in Hausa Na Gargajiya"},"content":{"rendered":"<p>Gabatarwa:<\/p>\n<p>Wa\u0199a dai ba ba\u0199uwar kalma ba ce. Tuni masana da manazarta suka yi caa a kanta wurin gudanar da bincike da rubuce-rubuce iri-iri a matakan ilimi daban-daban. Wannan ba ya rasa nasaba da yadda wa\u0199a ta kasance komai-da-ruwanka ga rayuwar Bahaushe da ma sauran al\u2019ummu duniya gaba \u0257aya. Bahaushe na yin cu\u0257anya da wa\u0199a a kusan dukkanin al\u2019amuransa na yau da kullum. Wannan ya ha\u0257a da siyasa da bukukuwa da wasanni da ilimantarwa da talla, kai har ma da wasu lamurran da suka shafi addini a wasu lokutan. Wannan kuwa ba ya rasa nasaba da yadda wa\u0199a ta kasance mai matu\u0199ar shiga jiki tare da kama zuciya da kuma jan hankali.<\/p>\n<p>Sai dai wa\u0199a ba ta kasance nau\u2019i guda ba kawai. A maimakon haka, akan samu sauye-sauye da kuma sabbin salailai da sigogin wa\u0199o\u0199i lokaci zuwa lokaci. Tun Bahaushe yana rera wa\u0199o\u0199insa da ka, har aka kai lokacin da ya fara rubuta su. Wannan ya faru bayan cu\u0257anyarsa da ba\u0199in al\u2019ummu musamman Larabawa da Turawa, wanda hakan ya samar masa da ilimin karatu da rubutu. Da tafiya ta yi tafiya kuma, sai zamani ya zo masa da sabon salon amfani da kayan ki\u0257an zamani domin rera wa\u0199o\u0199insa. Irin wa\u0257annan wa\u0199o\u0199in ne har yau ake kai-komo kan sunan da ya dace a ra\u0257a musu, musamman yadda suka kasance jemage, ba ka ga tsuntsu ba ka ga dabba. Wato dai suna \u0257auke da siffofin wa\u0199o\u0199in baka da kuma na rubutattun wa\u0199o\u0199i. Koma dai yaya abin yake, dole ne a yarda zamani ne ya zo da wannan tsari na wa\u0199a.<\/p>\n<p>A \u0253angare guda kuma, samuwar wa\u0199o\u0199in zamani na sutudiyo da kuma wasu nau\u2019ukan tasirin zammani a kan wa\u0199o\u0199in Bahaushe na gargajiya sun da\u0199usar da su wa\u0199o\u0199in gargajiyar, wanda har ta kai ga suna \u0199o\u0199arin \u0253acewa gaba \u0257aya. Wannan ne ya samar da bu\u0199atar yin wani yun\u0199uri domin tattara muhimman bayanai da za su adana wa\u0257annan nau\u2019ukan wa\u0199o\u0199i wuri guda domin gujewa salwantarsu. Wato dai ko da an wayi gari babu su a aikace, to kuwa za a ci gaba da tarar da su a rubuce, HAR MADI.<\/p>\n<p>Wannan littafi ya yi \u0199o\u0199arin tattara bayanai dangane da wa\u0199o\u0199in Bahaushe na gargajiya. An raba littafin zuwa babi-babi har guda takwas. Babi na farko ya kasance gabatarwa ne ga littafin. A cikin babin an waiwaici ra\u2019ayoyin masana dangane da asalin wa\u0199a. Baya ga haka, an kawo amfani ko muhimmancin wa\u0199o\u0199in na gargajiya. Daga ciki akwai fa\u0257akarwa da ilimantarwa da nisha\u0257antarwa da koyar da jarumta da talla da kuma addu\u2019ar alkairi da dai sauransu. Sannan kamar yadda Bahaushe ke cewa: \u201cKowane allazi da nasa amanu\u2026\u201d haka ma wa\u0199o\u0199in na da na\u0199asu ko koma baya. Wannan kuwa ya ha\u0257a da amfani da maganganun batsa ga wasu daga cikin wa\u0199o\u0199in.<br \/>\nBabi na biyu ya mayar da hankali ne kan wa\u0199o\u0199in wasanni. Wannan wani rukuni ne daga cikin rukunonin wa\u0199o\u0199in baka. Akan rera wa\u0199o\u0199i iri-iri yayin gudanar da wasanni daban-daban. Wa\u0257annan wa\u0199o\u0199i na zuwa da jigogi mabambanta wanda hakan ya danganta da lokaci da wurin wasan, da kuma masu gudanar da wasan da ma dalilin gudanar da shi. A cikin wannan babi na biyu, an kawo misalan wasannin da ke \u0257auke da wa\u0199o\u0199i. Daga ciki har da wasannin yara maza da na yara mata (wasannin ga\u0257a) da kuma wasannin tashe.<\/p>\n<p>Babi na uku kuwa, ya mayar da hankali ne kan wa\u0199o\u0199in aikace-aikace. Wannan ya fi shafar mata kai-tsaye. Nau\u2019ukan wa\u0199o\u0199i ne da mata ke rerawa yayin gudanar da ayyuka daban-daban. Irin wa\u0257annan wa\u0199o\u0199i na \u0257ebe musu kewa tare da \u0199ara musu kuzarin gudanar da aiki. Daga cikin irin ayyukan da akan rera wa\u0199a yayin gudanar da su akwai: Da\u0253e da sa\u0199a da kitso da daka da ka\u0257i da dai sauransu.<\/p>\n<p>A cikin babi na hu\u0257u, an kawo wa\u0199o\u0199in gargajiya da suka shafi aure ko raka amarya. Da ma dai, bukukuwan Bahaushe na cu\u0257anye da wa\u0199o\u0199i da kirare-kirare, ciki har da bukin aure. A yayin bukin aure, mata da \u2018yanmata na rera wa\u0199e-wa\u0199e, musamman ma lokacin da suke kan hanyar raka amarya \u0257akinta. Yawanci jigogin wa\u0257annan wa\u0199o\u0199i sun fi karkata kan bankwana ga amarya da tunasar da ita babban aikin da ke gabanta na zaman aure tare kuma da rarrashinta. Babin ya kawo jeranton misalai na irin wa\u0257annan wa\u0199o\u0199i.<\/p>\n<p>Babi na biyar kuwa, ya du\u0199ufa ne wurin kawo misalan wa\u0199o\u0199in cikin tatsuniya. Tatsuniyoyin Bahaushe sun kasance wani babban bagire da akan samu misalan wa\u0199o\u0199insa na gargajiya. Wa\u0199o\u0199in na da amfani cikin wa\u0257annan tatsuniyoyi ta fuskar fito da jigoginsu da suka ha\u0257a da fa\u0257akarwa da ilimantarwa da jarumta da dai makamantansu. Sannan wa\u0199o\u0199in sukan kasance \u0199arin gishiri ga wa\u0257annan tatsuniyoyi. Babin na biyar ya kawo misalan wasu daga cikin wa\u0199o\u0199in gargajiya na tatsuniyoyin Bahaushe.<\/p>\n<p>A babi na shida, an kawo misalan wa\u0199o\u0199in baka ne da suka shafi ro\u0199on ruwa. Wannan ma dai wani rukuni ne na wa\u0199o\u0199in bakan Bahaushe. Wa\u0199o\u0199in sun ha\u0257a da caccayya da Halilu da Allah mun tuba da dai makamantansu. A gaba kuwa, wato babi na bakwai, an kawo wa\u0199o\u0199i ne da suka shafi bara. Bara dai al\u2019ada ce da ta da\u0257e a \u0199asar Hausa. Mabarata na amfani da wa\u0199o\u0199in yayin gudanar da bararsu. Daga cikin irin wa\u0257annan wa\u0199o\u0199i akwai Saboda Manzon Allah da Mu Ro\u0199i Allah Sarki da makamantansu.<\/p>\n<p>Babi na takwas ya kasance na \u0199arshe a cikin littafin. Yana \u0257auke da bayanai kan siffofin wa\u0199o\u0199in gargajiya, tamkar dai yadda aka kawo misalan wa\u0199o\u0199in a babukan da suka gabata. Siffofin kuwa sun ha\u0257a da rashin tafiya da \u0199afiya ko \u0199arangiya da kasancewarsu ba su bu\u0199atar kayan ki\u0257a da dai makamantansu.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gabatarwa: Wa\u0199a dai ba ba\u0199uwar kalma ba ce. Tuni masana da manazarta suka yi caa a kanta wurin gudanar da bincike da rubuce-rubuce iri-iri a matakan ilimi daban-daban. Wannan ba ya rasa nasaba da yadda wa\u0199a ta kasance komai-da-ruwanka ga rayuwar Bahaushe da ma sauran al\u2019ummu duniya gaba \u0257aya. Bahaushe na yin cu\u0257anya da wa\u0199a [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"featured_media":11262,"comment_status":"open","ping_status":"closed","template":"","meta":[],"product_cat":[15],"product_tag":[211,210,212,209,208,213,70,192],"class_list":{"0":"post-11261","1":"product","2":"type-product","3":"status-publish","4":"has-post-thumbnail","6":"product_brand-alada-adabi","7":"product_cat-noma","8":"product_tag-adabi","9":"product_tag-aladun-hausawa","10":"product_tag-waoin-ayyuka","11":"product_tag-waoin-baka","12":"product_tag-waoin-gargajiya","13":"product_tag-waoin-tatsuniya","14":"product_tag-wikihausa","15":"product_tag-yadda-ake","17":"first","18":"instock","19":"sale","20":"downloadable","21":"shipping-taxable","22":"purchasable","23":"product-type-simple"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product\/11261","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product"}],"about":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/types\/product"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=11261"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/media\/11262"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=11261"}],"wp:term":[{"taxonomy":"product_cat","embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product_cat?post=11261"},{"taxonomy":"product_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product_tag?post=11261"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}