{"id":11249,"date":"2026-02-16T12:47:07","date_gmt":"2026-02-16T12:47:07","guid":{"rendered":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/?post_type=product&#038;p=11249"},"modified":"2026-02-16T12:47:07","modified_gmt":"2026-02-16T12:47:07","slug":"damfara-a-duniyar-intanet","status":"publish","type":"product","link":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/product\/damfara-a-duniyar-intanet\/","title":{"rendered":"Damfara A Duniyar Intanet"},"content":{"rendered":"<p>Wannan littafi ya yi bayani game da damfara a duniyar intanet. Ya kawo nau&#8217;ukan damfara daban-daban da \u0199warya-\u0199waryar bayanai game da yadda ake aiwatar da su. Bugu da \u0199ari, ya kawo hanyoyi da matakan da mutane za su iya bi domin kare kansu daga fa\u0257awa tarkon &#8216;yan damfara.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gabatarwa<br \/>\nDamfara hanya ce ta amfani da dabarun yaudara don kwa\u0257aitar da wani samun wani abin alfanu dangin ku\u0257i ko wani abu mai daraja, domin kar\u0253ar wani abu daga gare shi na dindindin. A \u0253angare guda kuwa, intanet fasaha ce ta zamani wadda ta \u0199unshi ha\u0257akar tsauraran al\u2019amura da suka ha\u0257a da yaruka da na\u2019urori da sabis wa\u0257anda ha\u0257uwarsu take samar da al\u2019amari ko bagire da yake tattare da hadahada da fannoni tamkar wa\u0257anda suke duniyar yau-da-kullum, ciki har da abubuwan da suka shafi sadarwa da makarantu da bankuna da kasuwanni da shaguna tare da sauran halittu kamar mutane da dabbobi da waninsu.<br \/>\nSamuwa da bun\u0199asar intanet a duniya ya bu\u0257e sabon babin damfara, wato damfara a duniyar intanet. Damfarar kan intanet ta fi shafar wa\u0257anda suke hawa intanet ta hanyar kafafen intanet ko na sada zumunta ko kuma manhajoji. A yau, akan dama da Hausawa da dama a duniyar intanet dangane da kasuwanci da sada zumunta da sauran abubuwan da suka shafi tura bayanai ko amfani da su a kan intanet. Hakan ya sa Hausawan suka shiga cikin jerin wa\u0257anda suke fuskantar \u0199alubalen damfara a kan intanet. Wannan ya sa ya zama dole a gudanar da binciken da zai fa\u0257akar da Hausawa game da matakan kare kai daga fa\u0257awa tarkon \u2018yan damfarar kan intanet.<br \/>\nLittafin yana \u0257auke da babuka guda shida (6). Babi na farko ya fara da bayani dangane da ma\u2019anar damfara. Daga nan ya kawo tsokaci game da ma\u2019ana tare da ta\u0199aitaccen tarihin samuwa da bun\u0199asar intanet. Babi na biyu kuwa ya mayar da hankali ne a kan tattauna batutuwan da suka shafi \u201cneman ku\u0257i a kan intanet.\u201d An fi mayar da hankali a kan nau\u2019o\u2019in kasuwanci da \u0199wadagon kan intanet wa\u0257anda suka shafi Hausawa. Babin ya bayyana cewa, masu gudanar da harkokin neman ku\u0257i a kan intanet sun fi fuskantar \u0199alubalen damfara.<br \/>\nBabi na uku kuwa ya tattauna nau\u2019o\u2019in damfara ta kan intanet daban-daban. Fahimtar ciki da wajen wa\u0257annan nau\u2019o\u2019in damfarar kan intanet wani muhimmin mataki ne na kare kai daga fa\u0257awa tarkon \u2018yan damfara. A babi na hu\u0257u, an tattauna wasu misalan manyan damfarar kan intanet da aka yi wa Hausawa, wa\u0257anda aka gudanar da su a cikin sigar kasuwanci. Hausawa masu yawa sun fa\u0257a wannan tarkon damfara inda aka yaudare su da sunan kasuwanci. Nazartar wannan babi zai taimaka wa masu karatu, musamman Hausawa, wajen na\u0199altar matakan tantance kasuwancin kan intanet na gaskiya da na bogi<br \/>\nBabi na biyar ya tattauna wasu fitattun misalan damfarar kan intanet da suka ritsa da Hausawa ta sigar kasuwancin ku\u0257in intanet (kirifto). An yaudari Hausawa masu yawa da wasu nau\u2019o\u2019in kirifto na damfara. Sun ha\u0257a da Insknation da Telegram P2P da AI Mining da sauran makamantansu. Bayanan da suke cikin wannan babin za su taimaka wa makaranta musamman Hausawa wajen bambance aya da tsakuwa, tsakanin harkokin kirifto na gaskiya da na damfara.<br \/>\nBabi na shida ya kawo wasu muhamman dabarun kare kai daga fa\u0257awa cikin tarkon \u2018yan damfara a kan intanet. Dabarun sun ha\u0257a da bayanai game da yadda ake gane sa\u0199onnin damfara da kafafen intanet na bogi. Haka kuma, sun shafi bayani game da muhimman matakai da ya kamata mutum ya \u0257auka domin kare akawun \u0257insa daga barazanar \u2018yan damfara. Akawun \u0257in yana iya kasancewa na kafafen intanet (websites da blogs) da manhajoji (applications) da kuma kafafen sada zumunta (social media).<br \/>\nMuna da ya\u0199inin cewa, wannan littafin zai yi matu\u0199ar taimakawa wajen fahimtar damfarar kan intanet da nau\u2019o\u2019inta da ma matakan kare kai daga wannan annoba ta damfara a kan intanet.<\/p>\n","protected":false},"featured_media":11250,"comment_status":"open","ping_status":"closed","template":"","meta":[],"product_cat":[76],"product_tag":[204,205,206,70,203],"class_list":{"0":"post-11249","1":"product","2":"type-product","3":"status-publish","4":"has-post-thumbnail","6":"product_cat-kimiyya-da-fasaha","7":"product_tag-damfara","8":"product_tag-kasuwanci","9":"product_tag-sanaoi","10":"product_tag-wikihausa","11":"product_tag-zamani","13":"first","14":"instock","15":"sale","16":"downloadable","17":"shipping-taxable","18":"purchasable","19":"product-type-simple"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product\/11249","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product"}],"about":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/types\/product"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=11249"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/media\/11250"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=11249"}],"wp:term":[{"taxonomy":"product_cat","embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product_cat?post=11249"},{"taxonomy":"product_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product_tag?post=11249"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}