{"id":11246,"date":"2026-02-16T12:09:20","date_gmt":"2026-02-16T12:09:20","guid":{"rendered":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/?post_type=product&#038;p=11246"},"modified":"2026-02-16T12:09:20","modified_gmt":"2026-02-16T12:09:20","slug":"hausa-da-hausawa-a-duniyar-intanet","status":"publish","type":"product","link":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/product\/hausa-da-hausawa-a-duniyar-intanet\/","title":{"rendered":"Hausa Da Hausawa A Duniyar Intanet"},"content":{"rendered":"<p>Wannan littafi yana \u0257auke da bayanai game da yadda ake samun harshe da al&#8217;adu da adabin Hausawa a duniyar intanet. Ya kuma kawo bayanai game da tasirin intanet kan rayuwar Hausawa da rawar da Hausawa za su iya takawa domin cin gajiyar intanet a yau.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gabatarwa<br \/>\nX.1 Matashiya<br \/>\nWannan littafin ya \u0257auki intanet a matsayin \u201cduniya\u201d mai zaman kanta. A ciki (duniyar) akan tarar da duk wa\u0257ansu al\u2019amura na yau da kullum suna gudana tamkar yadda suke kasancewa a duniyar zahiri. A duniyar intanet akan sami \u0257ai\u0257aikun mutane (akawun-akawun da kafafen intanet na \u0257ai\u0257aikun mutane). Akan kuma sami unguwanni (zauruka da kafafen intanet na tarayya). Ana kuma samun garuruwa da \u0199asashe. Al\u2019amuran da suke gudana a kowane daga cikin \u0253angarorin sun kasance tamkar a duniya ta daban wadda ta kai ta dogara da kanta. A duniyar intanet, akan:<br \/>\na. samu cinikayya da kasuwanci suna gudana tamkar yadda ake yi a duniyar zahiri ta mutane (kasuwanni da shaguna da dillalai da makamantansu);<br \/>\nb. samu zamantakewa da rayuwa mai kama da mafarki. Misali, ana iya samun tarayya tsakanin al\u2019ummomi daga \u0253angarorin duniya wa\u0257anda ba su ta\u0253a kallon juna a zahiri ba;<br \/>\nc. samu makarantu da azuzuwa har da \u0257akunan karatu\u2019<br \/>\nd. samu gine-gine da wurare da sauran abubuwan amfani masu matsayi kwatankwacin abubuwan amfanin bil\u2019adama ta rayuwar zahiri.<br \/>\nWato dai, al\u2019amuran suna kasancewa cikin siga da salo makamanciyar yadda suke a duniyar zahiri. Akan kuma samu cu\u0257anya tsakanin al\u2019amuran da suke wanzuwa a duniyoyin guda biyu. Daga duniyar zahiri ne ake samun damar cu\u0257anya da duniyar intanet ta hanyar na\u2019urori. Wasu lokutan akan kai ga dawo da gudanarwar cu\u0257anyar zuwa duniyar zahiri. Misali, soyayyar duniyar intanet ta Isa Suleiman Fanshekara (\u0257an Kano a Nijeriya) da Ba\u2019amurkiya Janine Sanchez ta zama gaskiya. Don \u0199arin bayani a duba BBC, (2020 para. 1)2 ko Abubakar, (2020 para. 1).<br \/>\nBabban al\u2019amari kuma shi ne, akan rayu kuma a mutu a duniyar intanet. A rahoton da BBC ta fitar bayan bincike kan Fesbuk a shekarar 2016, ta bayyana kafar Fesbuk a matsayin wata babbar ma\u0199abarta. Rahoton yana da taken: \u201cYadda Facebook ya zama makekiyar ma\u0199abarta.\u201d An tabbatar da cewa, shekaru takwas (8) kacal bayan bu\u0257e Fesbuk, an samu masu amfani da kafar da suka mutu kimanin miliyan talatin (30,000,000). A bisa wannan, ana iya hasashen cewa ya zuwa yau adadin ya ninninka sau tarin yawa. Tun a shekarar 2012, adadin masu amfani da Fesbuk da suke mutuwa a kowace rana ya kai dubu takwas (8,000) (BBC, 2016 para. 1). Hakan yana nuni da cewa, adadin zai ci gaba da hauhawa yayin da ake samun \u0199aruwar masu amfani da kafar.<br \/>\nHa\u0199i\u0199a akwai bu\u0199atar a samu jakadu da wakilan Hausa da Hausawa a duniyar intanet, tamkar yadda ake da su a duniyar zahiri. Wannan littafi sharar fage ne da zai bu\u0257e hanyar samar da wakilcin al\u2019adun Hausa a duniyar ta intanet.<br \/>\nX.2 Madogaran Littafin<br \/>\nWannan littafi ya ta\u0199aita ne a kan al\u2019adun Hausawa da intanet. Kadadarsa ba ta wuce duniyar intanet ba. Ko a duniyar intanet \u0257in ba ko\u2019ina aka duba ba. Littafin ya ta\u0199aita a kafafen intanet na Hausa kawai. Dangane da sauran kafafen intanet, an yi \u0199o\u0199arin duba al\u2019adun Hausawa ne kawai daga cikinsu tare da nazartar irin tasirin da suka yi a kan al\u2019adun Bahaushe. Ma\u2019ana ke nan, an bibiyi kafafen domin ganin abin da suke fa\u0257a ko suke nunawa dangane da al\u2019adun Hausawa. An cim ma nasarar hakan ta hanyar:<br \/>\ni. nazartar rubuce-rubucen;<br \/>\nii. nazartar hotuna;<br \/>\niii. nazartar bidiyoyi; da<br \/>\niv. nazartar alamomi.<br \/>\nBa a iyakance adadin kafafen intanet da aka dubo wa\u0257annan ba. Dalili kuwa shi ne, ya zuwa yau (2020), akwai kafafen intanet a duniya da adadinsu ya haura biliyan \u0257aya da miliyan \u0257ari bakwai da hamsin da \u0257aya da dubu talatin da \u0257aya da \u0257ari hu\u0257u da arba\u2019in da bakwai (1,751,031,447) (Internet Live Stats, 2020 para. 2). Za\u0253en wasu tsiraru daga cikin kafafen intanet \u0257in na iya sa a tsallake wasu muhimman abubuwa da suka dace a yi magana a kansu. Hakan zai faru idan fitilar nazari ba ta haska kafafen intanet da suke \u0257auke da wa\u0257annan bayanai ba. A \u0253angaren tasiri kuwa, za a yi \u0199o\u0199arin gano irin gurbin kafafen na intanet ga rayuwar Bahaushe, musamman al\u2019adunsa.<br \/>\nDangane da wa\u0257annan kafafen intanet na Hausa, an mayar da hankali ne a kan abin da ya shafi al\u2019adu kawai. A cikin kafafen, za a yi \u0199o\u0199arin za\u0199ulo al\u2019adun Hausawa da suka shafi:<br \/>\ni. nazarin inda aka fito dangane da adanawa da yayata al\u2019adun Hausawa a duniyar intanet;<br \/>\nii. nazarin matsayin da al\u2019adun Hausawa suka tsinci kansu a yau cikin wa\u0257annan kafafen intanet na Hausa;<br \/>\niii. nazarin matsaloli ko barazanar da al\u2019adun Hausa suke fuskanta a duniyar intanet; da<br \/>\niv. nazarin hanyoyi ko matakai da za a iya inganta kafafen.<br \/>\nX.3 Babukan Littafin<br \/>\nWannan littafin yana \u0199unshe da babuka guda biyar. Babi na \u0257aya ya kasance shimfi\u0257a ne. A ciki an waiwaici samuwa da bun\u0199asar intanet. Bugu da \u0199ari, babin ya yi bitar kalmar \u2018al\u2019ada\u2019 domin yin matashiya ga littafin. Bayan haka, babin ya dubi irin tasirin da intanet yake da shi a kan al\u2019ummomi a duniya.<br \/>\nAn gina babi na biyu a kan bun\u0199asar al\u2019adun Hausawa a duniyar intanet. Babin ya duba manyan kafafen intanet a duniya da suka kar\u0253i harshen Hausa. Daga cikinsu har da Fesbuk. Bugu da \u0199ari, babin ya kalli ire-iren tasirin da intanet yake da shi ga Hausa da kuma Hausawa.<br \/>\nBabi na uku ya mayar da hankali a kan nazarin ya\u0257uwar al\u2019adun Hausawa a kan intanet. A ciki an duba yadda al\u2019adun Hausawa daban-daban suka ya\u0257u a kan intanet. Sukan bayyana yayin da aka tura neman da yake da ala\u0199a da su a cikin injunan nema na kan intanet.<br \/>\nA cikin babi na hu\u0257u, an nazarci amfani da aibun intanet ga Hausa da Hausawa. Ya tabbata cewa, intanet ya zo da alfanu masu tarin yawa wa\u0257anda Hausa da Hausawa za su iya cin gajiyarsu musamman yayin da suka bi hanyoyin da suka kamata. Daga cikin amfaninsa akwai ba da damar sada zumunta da ha\u0253aka Hausa da yayata ta. Yana kuma taimakawa wajen adana al\u2019adun Hausawan. Aibin kafafen intanet ga al\u2019ummar Hausawa sun ha\u0257a da \u0253ata tarbiyya da \u0253ata lokaci da samar da kafar damfara da makamantansu. A \u0253angare \u0257aya kuwa, intanet ya zo da \u0199alubale daban-daban wa\u0257anda dole sai an bi kyawawan matakai domin kauce musu.<br \/>\nBabi na biyar ya tattauna nasarorin da kafafen intanet na Hausa suka samu a yau. Wannan ya ha\u0257a da \u0199aruwar \u0199arfin tasirinsu a duniya da fannonin rayuwa da suka mamaye, ciki har da kasuwanci da ilimi. A \u0253angare \u0257aya kuwa, babin ya kawo wasu \u0199alubale da kafafen suke fuskanta. Sun ha\u0257a da \u0199arancin tallafi da goyon baya daga masana da mahukunta da kuma wasu matsaloli da suka shafi yanayi da zamantakewar \u0199asar Hausa.<\/p>\n","protected":false},"featured_media":11248,"comment_status":"open","ping_status":"closed","template":"","meta":[],"product_cat":[76],"product_tag":[202,168,70,203],"class_list":{"0":"post-11246","1":"product","2":"type-product","3":"status-publish","4":"has-post-thumbnail","6":"product_cat-kimiyya-da-fasaha","7":"product_tag-intanet","8":"product_tag-kimiyya","9":"product_tag-wikihausa","10":"product_tag-zamani","12":"first","13":"instock","14":"sale","15":"downloadable","16":"shipping-taxable","17":"purchasable","18":"product-type-simple"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product\/11246","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product"}],"about":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/types\/product"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=11246"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/media\/11248"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=11246"}],"wp:term":[{"taxonomy":"product_cat","embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product_cat?post=11246"},{"taxonomy":"product_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product_tag?post=11246"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}