{"id":11211,"date":"2026-02-11T11:07:54","date_gmt":"2026-02-11T11:07:54","guid":{"rendered":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/?post_type=product&#038;p=11211"},"modified":"2026-02-11T13:17:14","modified_gmt":"2026-02-11T13:17:14","slug":"wasannin-kwaikwayo-na-hausawa","status":"publish","type":"product","link":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/product\/wasannin-kwaikwayo-na-hausawa\/","title":{"rendered":"Wasannin Kwaikwayo Na Hausawa"},"content":{"rendered":"<h1>GABATARWA<\/h1>\n<p>Ha\u0199i\u0199a, wasannin kwaikwayo na gargajiya sun kasance wani \u0253angare na rayuwar \u0257an\u2019adam. Wannan kuwa bai tsaya a kan Hausawa ba kawai, ya shafi dukkanin al\u2019ummun duniya da ke \u0199asashe daban-daban. Sai dai akan sami bambance-bambancen salo da siga na wa\u0257annan wasanni, wanda hakan ya danganta ga al\u2019ada da yanayin wurin zama na masu wannan wasa.<\/p>\n<p>Wasannin kwaikwayon da Hausawa suka gada tun iyaye da kakanni na fuskantar dusashewa, tamkar dai sauran al\u2019adun Hausawan. Wannan na faruwa ne sakamakon dalilai masu dama wa\u0257anda za a iya ta\u0199aita su da furucin <em>tasirin zamani.<\/em> Lura da wannan \u0199o\u0199arin \u0253acewa da mafi yawan wasannin kwaikwayo na gargajiya ke yi, akwai bu\u0199atar killace su wuri \u0257aya a matsayin wani kundin da zai kasance abin waiwaiya a kodayaushe. Yin hakan zai sanya ko da wasannin kwaikwayon sun gushe a zamani, za su kasance a killace har Madi.<\/p>\n<p>Marubutan wannan Littafin sun tattara wasannin gargajiya na Hausawa guda \u0257ari biyu da goma shahu\u0257u (214) a shekara ta 2021. Sun wallafa su a cikin littafi mai suna <em>Wasanni a <\/em><em>\u0198<\/em><em>asar Hausa. <\/em>Littafin ya \u0199unshi dukkannin nau\u2019ukan wasanni \u2013 na kwaikwayo da wa\u0257anda ba na kwaikwayo ba. Daga baya ne suka yi tunanin ware wasannin kwaikwayo daga cikinsu. An yi nasarar ware wasannin kwaikwayo guda 50.<\/p>\n<p>An raba littafin zuwa babuka shida (6). Babi na farko yana \u0257auke da gabatarwa. A ciki an kawo bayani game da ma\u2019anar wasan kwaikwayo. An kuma kawo amfanin wasannin kwaikwayo da rabe-rabensu. Babi na biyu zuwa na biyar kuwa na \u0199unshe da bayanai game da wasannin kwaikwayo na gargajiya daban-daban. Sun ha\u0257a da na yara maza da yara mata da na tarayya. A gefe guda kuwa, an kawo na manya maza da mata. Babi na shida wanda shi ne na \u0199arshe, yana \u0199unshe da bayani game da tasirin zamani a kan wasannin kwaikwayon Bahaushe na gargajiya.<\/p>\n<p>Bayan an kawo jerin manazarta, sai kuma aka biyo baya da ratayen wa\u0257annan wasannin kwaikwayo na gargajiya cikin tsararren jadawali. An yi hakan ne domin samar da haske ga mai karatu ko bincike, yadda zai samu bayanai masu muhimmanci a kan kowane wasa kai tsaye. Ga kowane wasa, an bayyana abubuwa da suka ha\u0257a da:<\/p>\n<ol>\n<li>Sunan wasa<\/li>\n<li>Masu wasa<\/li>\n<li>Rukunin wasa<\/li>\n<li>Kayan aiki<\/li>\n<li>Amfanin wasa<\/li>\n<\/ol>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Wannan littafi yana \u0257auke da bayanai tare da misalan wasannin kwaikwayo na Hausawa. Yana \u0257aya daga cikin littattafan da WAEC suka kar\u0253a domin sakawa a makarantun sakandare.<\/p>\n","protected":false},"featured_media":11216,"comment_status":"open","ping_status":"closed","template":"","meta":[],"product_cat":[74,158],"product_tag":[191,190,70,192],"class_list":{"0":"post-11211","1":"product","2":"type-product","3":"status-publish","4":"has-post-thumbnail","6":"product_cat-tarihi","7":"product_cat-waka","8":"product_tag-hausawa","9":"product_tag-wasannin-kwaikwayo","10":"product_tag-wikihausa","11":"product_tag-yadda-ake","13":"first","14":"instock","15":"sale","16":"downloadable","17":"shipping-taxable","18":"purchasable","19":"product-type-simple"},"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product\/11211","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product"}],"about":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/types\/product"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=11211"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/media\/11216"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=11211"}],"wp:term":[{"taxonomy":"product_cat","embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product_cat?post=11211"},{"taxonomy":"product_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/wikihausa.com.ng\/littattafai\/wp-json\/wp\/v2\/product_tag?post=11211"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}