fbpx
Friday, June 2, 2023
Home Littattafai Waƙa Waiwaye Kan Harshen Makaɗi A Zubin Waƙar Baka

Waiwaye Kan Harshen Makaɗi A Zubin Waƙar Baka

0.00

Description

Waiwaye Kan Harshen Makaɗi A Zubin Waƙar Baka

Daga: Sa’idu Muhammad Gusau, Jami’ar Bayero, Kano

Gabatarwa

Baiwa ta naƙaltar harshe da iya samarwa da sarrafa kalmomi a tsari da ɗabi’ar al’umma hanya ce wadda take ba da dama a shirya waƙoƙi kuma a rera wa jama’a. Mutum yakan zama makaɗi a lokacin da ya mallaki baiwa ta shirya kalmomi cikin saɗaru; sannan ya kasance yakan tsara waƙoƙi lokaci bayan lokaci har al’umma ta gane ya iya waƙa; a san shi da yin waƙa, kuma ya zama mai adani da kiyaye alfarmar waƙa; tare da ba waƙar kulawa da kima a matsayinta na adabi mai shirya al’umma.

×