fbpx
Monday, September 25, 2023
Home Littattafai Hausa Novels Rayuwa Da Ƙarfafa Ilimi Da Makarantunsa Da Wasu Hidimomin Rayuwa A Zukatan Zamfarawa A Jihar Zamfara

Rayuwa Da Ƙarfafa Ilimi Da Makarantunsa Da Wasu Hidimomin Rayuwa A Zukatan Zamfarawa A Jihar Zamfara

0.00

Description

Zamfarawa mutane ne waɗanda suka shahara da mazauni a ƙasar Hausa; kuma suka samar da Daular Zamfara wadda ta wanzu tun kafin ƙarni na goma sha huɗu (14). Ƙasar Zamfara ta zauna a ƙarƙashin jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo (1804-1903); sannan ta kuma zauna a farfajiyar yankin Arewa. Haka kuma ƙasar Zamfara ta taɓa zaunawa a ƙarƙashin Jihar Arewa masu Yamma ta Sakkwato tun daga 1967; kuma tun 1976 wasu gundumomi na yankin Zamfara suka zama ƙananan hukumomi. Kuma Zamfara ta koma a sabuwar Jihar Sakkwato a shekarar 1991; sannan a 1996, ranar Alhamis 1/10/1996 ta zama Jiha mai cin gashin kanta.

Daular Zamfara, Daula ce wadda ta wanzu a ɓangaren Nijeriya ta Arewa wadda kuma ta Mallaki faɗin ƙasa wanda ya kama daga Kogin Rima a sashen Arewa zuwa Gulbin Zamfara a Jihar Kudu. Ta fuskar Gabas kuwa Daular Zamfara ta yi iyaka da Dajin Rugu zuwa Dutsin Disau a Yamma (Gusau, B.M & Gusau, S.M. 2012: 20-20).

×