fbpx
Tuesday, June 6, 2023
Home Littattafai addini Ladaban Zama Da Kishiya A Musulunci

Ladaban Zama Da Kishiya A Musulunci

0.00

Domin karanta littafin, danna koren rubutun nan.

Ladaban Zama Da Kishiya A Musulunci

Description

Ya ‘yan uwa Musulmai, mu sani cewa, mun shigo wani zamani, wanda duk wani tsari, wanda Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ɗora mu a kai ƙoƙari ake yi sai an kawar da mu daga kansa, an ɗora mu a kan tafarkin Nasara, ko ma na Yahudu.

Mu sani cewa tun daga tsarin ilimi, tsarin Zamantakewa, tsarin Tattalin Arziki, tsarin shari’ah zuwa uwa-uba, tsarin Siyasa, duka an fa kawar da mu daga abinda Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ɗora mu akai. Yanzu abin da yake faruwa shi ne; ana son lallai sai an haramta mana auren mace sama da ɗaya; wanda yake cikin tsarin zamantakewar mu ta musulunci. Alhali an buɗe ƙofa hanhai ta daɗa lalacewa, ta ma ruguje baki ɗayanta.

Auren mace daga ɗaya zuwa huɗu abu ne halattacce a addininmu, ga wanda yake da hali, kuma ya tabbatar zai yi adalci a tsakaninsu. Amma yanzu da yawa daga cikin Musulmai suna neman su kauce wa wannan hanya; saboda wasu dalilai. Dalilin kuwa ba su wuce tsoron talauci ko zafin kishi, daga ɓangaren mata ba. Mu sani cewa; duka waɗan nan ba dalilai ba ne masu ƙarfi.

×