Description
Haƙiƙa Allah Ta’ala ya girmama ɗan adam ya yi masa baiwa mai yawa; ya tsara masa komai ta yadda zai zama shugaba kuma mai sarrafa duk abinda yake bayan ƙasa na dabbobi; tsirrai, ma’adanai da dukkan albarkatu na ruwa da na tudu da na ƙarƙashin ƙasa.
Wannan shine ma’anar halifancin da Allah ya halicci mutum ya zaunar da shi a wannan duniyar dominsa.