Description
Shimfiɗa
Ibnu Qayyim al-Jauziyyah (Allah ya masa rahama) yana cewa:
“Mafi girman falalar abin da rai zai samu, zuciya za ta riska, bawa zai samu daraja da ɗaukaka a duniya da lahira shi ne Ilimi da Imani”2.
Haɗuwar Ilimi mai amfani da Imani ingantacce su ne turaku guda biyu.
Na asalin samun aiki nagartacce da arziƙi mai ɗorewa a wannan taƙaitacciyar rayuwar duniyar da dauwamammiyar rayuwar lahira.