fbpx
Sunday, March 26, 2023
Home Littattafai Tarbiya ALHARBU KHUD’ATUN

ALHARBU KHUD’ATUN

0.00

Takaitaccen nazari da fahimta akan fadin manzon Allah (saw)
“ALHARBU KHUD’ATUN” watau a ma‟ana YAKI DAN DABARA NE
wanda na sami damar nazarta da fadada fahimta a kai bayan na
halarci darasin mako-mako na Riyadus-salihina a ranar Tara ga
watan Rajab 1443-AH (10th February 2022) a karkashin KitabulJihaad wanda Dr.malam Aminu Ismai‟l sagagi ke gabatarwa a
kowace alhamis tsakanin Magriba zuwa Isha‟i a masallacin Ubaibin-ka‟ab da ke UDB Road, Kano.

Description

Dukkanin yabo da godiya da girmamawa sun tabbata ga Allah
subhanahu wa ta‟ala. Mai iko akan komai wanda ya kaddara komai
akan yadda yake so. Gaisuwa da salati sun tabbata ga manzon
Allah sallahu alaihi wa sallam. Mafificin Ambato a cikin dukkan
halittu.
Bayan haka, ina so inyi amfani da wannan dama domin fashin baki
da ta‟aliki akan wannan maudu‟i na “ALHARBU KHUD’ATUN”
ma‟ana yaki dan dabara ne ta yadda zamu iya fadada ma‟anar sa
da kuma alakanta ta acikin dukkan al‟amuran mu na rayuwa
domin samun gagarumar nasara da rayuwa mai tsafta a dukkan
mu‟amalar mu ta yau da gobe.
Hadisi ne ingatacce (1) daga manzon Allah (saw) cewa “ALHARBU
KHUD’ATUN” wato yaki dan Dabara ne ko kuma yaki dan yaudara
ne ko kuma yaki dan bazata ne.
Abin da ake nufi anan da yaki dan Dabara ne shine, amfani da
dukkan salon na hikima ko dabara don karya lagwan abokin gaba
a lokacin yaki ko kuma kafin yaki.
Haka, manzon Allah (saw) yayi amfani da wannan salon a wurare
daban daban yayin yaki don karya lagwan abokan gaba. Misali,
lokacin yakin badar, gaggawa zuwa badar domin mallakar rijiyar
badar wadda ita kadai ce rijiya dake iya samar da ruwa a wajen.
Haka a yakin uhud da sauran yakukuwan manzon Allah (saw) an yi
amfani da dabarun yaki na salon hikima don jefa razani da firgici a
kirazan abokan gaba kuma hakan ya yi matukar tasiri sosai wajen
samun nasara ga musulmi.
Wannan kenan, kamar yadda na ambata a sama, wannan shine
salon gudanar da sha‟nin yaki da musulunci yayi riko dashi. Kuma
a duk hikimar da addini yazo dashi don cimma wata manufa, ana
iya amfani da wannan hikima don cimma dukkan manufofi a
rayuwa.
Makasudin kawo wannan misali na yaki a sama, shine, wannan
kalma “ALHARBU KHUD’ATUN” wato yaki dan Dabara ne muna
iya aiki da ita a kowane bangere na rayuwar mu don cimma mafita
ga matsalolin da suke addabar mu cikin zamantakewar mu da
ma‟amalolin mu na yau da kullum. Misali idan muka dauki cewa
matsalolin mu sune yakin da muke tinkara kuma muka dauki cewa
“Dabara” itace salon da za mubi mu tinkari wannan matsala,
tabbas za mu ci gagarumar nasara wajen magance dukkan
matsalolin mu, ba tare da mika korafi ga gwamnati ko wasu
mahukunta ba.

1 review for ALHARBU KHUD'ATUN

  1. Husaini Inuwa

    best book ever

Add a review

Questions and Answers

You are not logged in

×