Komai Ya Yi Tsanani

0
150

KOMAI YAYI TSANANI……

Tana zaune a barandar gidansu ta haxa kai da gwiwa, kuka take yi sosai.
Shin yaushe zan bar gidan nan don in huta wannan halin uqubar da
nake ciki? Ni da gidan ubana, amma sam bani da jin daxi saboda kawai
ni marainiya ce.
Oh! Allah ka kawo min dauqi ya Allah, tabbas maraici abu ne mai ciwo, duk da
dai a musulunci ba za ta kira kanta da marainiya ba, saboda mahaifinta yana nan da
ransa.
sai dai zata iya cewa shi xa babu bambancin kaxan ne don bai iya tavuka komai
a gidannsa ba, duk irin so da qaunar da yake mata yana ji yana gani ake musguna
mata, shin menene abun yi?
Yaya Muhammad da yaya rahma yanzu kuna gani na a wannan halin kun kasa
xaukar wani matakin akai? Tabbas da wanda ya mutu yana dawowa in innarmu ta
dawo ta iske ni a wannan hali sai tayi tir da haihuwarku, musamman ke yaya
Rahma.
Gara Muhammad bai san halin da ake ciki kamar ke ba, duk da tasan yayar tata
tana jin takaicin halin da take ciki, sai dai ba za ta iya yin wani abu akai ba, to uban
nasu ma yana kallo ya kasa Magana balle kuma ita.
Addu’a ne tana yi mata allah ya fiddo mata miji tayi aure ko zata huta da wannan
halin da take ciki.

To idan auren ma zata yi waye zai aure ta a haka da take kamar yar aik, kullum
tana cikin aiki kullum tana cikin kayan tsumma, wane namiji ne zai yi sha’awar
aurenta a haka? Kai da wuya. To amma ta miqa wa Allah lamrinta, don tasan
komai yayi tsanani sauqi zai zo.
Ji tayi an dafata ta baya , tax ago kanta da sauri. Aisha ta gani
“Haba Asma’u! yaushe za ki daina sanya ranki cikin damuwa, shin ban ce miki ki
cire damuwa a ranki ki miqa lamarinki ga Allah ba? Na sha gaya miki Asma’u
komai yayi tsanani sauki zai zo da yardarm Allah.”
Hawaye na bin kumatunta ta ce, “Haba Aisha, don kawai babu ran mahaifiyata sai
aunty ta dauki tsangwama ta dora min ko tausayin halin da nake ciki bata yi ba.Ki
duba ta kori yan aikin gidan nan, ni ke komai, makaranta sai nayi da gaske nake
zuwa, jiya juma’a wallahi test ne damu amma qiri-qiri ta hana ni zuwa.
Aisha cikin tausayawa ta ce, “Asma’u irin wadannan matan ne suke bani mamaki,
ke kina mace kina haihuwa ko in ce kin Haifa amma ki dinga wulaqanta yar
kishiya, alhalin kema kin Haifa ba ki san yanda rayuwarki zata kasance nan gaba
ba. Za ki iya rasuwa kea ki bar wa wani yarki, shin in an wahalar da ita za ki ji
daxi?
Asma’u ta share hawayen idonta, t ace “sam aunty ba ta tunanin zata mutu, da
kuwa tana tunanin mutuwa wani abun ba zata yi shi ba, ki duba ki ga yanda take
juya baba tamkar mijin shi ne matar, ke dai Allah ya kyauta.”
Washegari da wuri ta soma aikin gidan, qarfe tara diadai ta gama komai komai,
tayi wanka. Doguwar rig ace ajikinta na atamfa, duk an haxu a falo ana karyawa,
amma ita tana gefe da dumaman tuwon jiya tana ci.
Alh. Abdullahi ya kasa cin haxaxxen break fast xin da ke gabansa, saboda duk
hankalinsa yana kan yar marainiya da aka tura mata xumame sai ka ce ba yar gida
ba. Ai ko mai aiki aka yi wa haka ai ba ayi mat adalci ba, balle yarshi kuma shi ya
nemo abincin nan da guminsa. Amma kuma bai da halin Magana.

Na’ima sai kallon mahaifiyarsu take tana jiran ta xan matsa ta xebawwa
Asma’u bread da qwai da suke karyawa dashi, sai dai yau uwar ta ki matsawa balle
ta samu dammar bata.
Sarauniyar Haj. Zainab ta dubi maigidan t ace “Alhaji naga ba ka karyawa ka tsaya
kana tunani.”
Ya dub eta, sannan ya xan yi qarfin halin cewa , “Hajiya lamrin yarinyar nan
ne yake dammu na, kalli abin da muke karyawa das hi amma ita dube ta can rave
xumamen tuwon jiya ne take ci.
Shin mun yi mata adalci? Allah fa zai….” Ta katse shi da sauri. “Tsaya –tsaya
kada ka ishe ni, ban hanata cin wannan ba, ai ita ta haxa komai amma ta rage sai ta
xauka.”
Asma’u da ke gefe hawaye masu zafi suka dira akan kuncinta, in da sabo ya
isa ace ta saba da halin Haj. Zainab, sai dai ita yanzu yanda take dakawa
mahaifinsu tsawa ko a gaban waye shi yafi damunta.
Shi yasa taji ta tsaneta bata tava tsanar mutum irin yanda ta tsani auntyn ba,
gani take da za a bata wuqa zata iya kashata har lahira saboda irin su a ganinta
annoba ce a cikin mutane.
“Au, ka fasa karyawar tunda ba a bai wa ‘yar gaban goshinka ba ? To wallahi
kaja mata, ko dam un rage ba za ta ci shi ba.” Ta miiqe ta bishi har xakinsa tana ci
gaba da masa maganganu masu zafi.
Na’ima kamar dama jira take yi, ta nufo Asma’u da break fast xinta ma ba
wani ci tayi sosai ba, saboda duk hankalinta na kan ‘yar ywarta. Nuratu ta ce “Au,
kai ka yi. Sai mun gayawa Aunty.
Ko kallonta ba ta yi ba ta miqe tana kuka ta shiiga xakinta.
Alhaji Abdullah hamshaqin mai kuxi ne, asalinsa xan garin katsina ne, babban mai
‘ya’ya yanzu haka yake karatu a qasar (London).

Sai kuma Rahma wadda shekararta huxu Allah yayi wa mahaifiyarsu rasuwa.
Alh. Abdullah ya shiga tashin hankali marar misaltuwa saboda yana tsananin son
matarsa sa’adatu.
Wannan yasa ya jima bai yi aure ba, ya xebi ‘ya’yan ya kaisu gun
mahaifiiyarsa. Said a Haj Sa’adatu ta shekara bakwai da rasuwa sannan ya koma
yin aure, da takurawar ‘yan uwansa don a da cewa yayi ba shi ba aure don ba zai
tava samun kamar sa’adatu ba.
Haj. Zainab ‘yar abokin Babansa ne, mahaifinsa ya matsa masa lallai sai yaje ya
nemeta, ba a daxe ba suka sasanta aka yi auren, tun shigowarta ta lira da irin son da
yake yi auren, tun shigowarta ta lura da irin son da yake yi wa matarsa, wannda
yanzu ya koma kan ‘ya’yansa.
Ai kuwa ta xaga hankalinta akan lallai sai ya kawo mata ‘ya’yansa ita ta riqe.
Ba wani abu ne yasa t ace haka ba, sai don ganin yanda yake yawan yi musu
hidima, komai kyaji ya ce ‘ya’yansa, musamman ma Asma’u wadda ta fi
shiga ransa saboda tsananin kamarta da mahaifiyarta.
Ganin ya qi yarda ya bata riqonsu yasa ta haxa masa da malamata da
Bokaye, da kansa yaje ya xauko su ya kawo su. Ran mahaifiyarsa ya vaci sosai, to
amma said a ya tura Muhammad (London) karatudon dama y agama (secondary).
Ita kuma Rahama tana (S.S.2), kuma dama da mai sonta an saka rana jira ake ta
kamala karatunta. Gaba xaya watan Rahma goma a gida aka sha bikinta, aka kai ta
zariya. Sai Asma’u ce kawai ta rage.
Ba yanda inna larai bat a yi ba Alhaji ya bar mata Asma’u yar shekara goma
cib ya qi, dalilin kenan riqonta yake hannun matar Babanta Haj. Zainab. Tun
lokacin take bala’in bata wuya babu wanda bai sani ba a kaf danginsu, sai dai ba
ka isa kayi Magana ba.
Duk zuwan da rahma tayi sai ta yi wa ‘yar uwarta kukan halin da take ciki, ta
sani koda ta tambayi a bata riqon ‘yar ba zai bata ba, tunda mahaifiyarsa ma tayitayi ya qi badawa, balle kuma ita. Dangin innarsu ma sun ta yi ya qi badawa, dole
suka qyale shi.

Duk unguwar babu wanda bai tausayin Asma’u, duk xinbin dukiyar mahaifinta
amma tana cikin uquba a gidansa, da kuma ransa. Kai! Mata muji tsoron Allah,
duniya fa ba matabbata b ace.
A cikin Hotoro G.R.A suke, duk cikin jerin gidajen babu gidan da ya kai gidan
Alh. Abdullah kyau da tsaruwa, wata haxaxxiyar mota c eta fito daga cikin gidan,
Asma’u ce ta biyo ta da gudu.
Alhaji yace “Tsaya-tsaya kamar Asma’u ce ke bin mu ko? Eh, itace. Bayan
yayi parking ta qaraso gurin motar abban nata ya buxe ta sanya masa kuka, ya
jawo ta kansa ta xora kanta akan cinyarsa, kuka take yi sosai hannaunsa akan ta
yana shafa gashin kanta.
shima idanuwansa duk sun canza launi kamar zai yi kuka, sai dai ya daure. Don bai so ta ga xigon
hawayensa. Direba da ka kallon duk abin da ke faruwa, shima ji yake kamar yasa kuka, yasan komai daga
halin da Asma’u take ciki, shima yana bayan masu tausaya mata.
Shi kam ba don yana ganin tafi qarfinsa ba da ya aure ta, don kawai ya tsame ta daga halin da take
cikiyasan duk da ba wani qarfi ne shi ba, zaman gidansa zai fi mata zaman da take yi yanzu.
To shi ina wannan maganar tunda shi direba ne a gidansa tafi qarfinsa, duk da cewa shima
matashin saurayi ne wanda gaba xaya shekarsa ashirin da tara, karatu ne yayi sai dai rashin aiki shi yasa
ya vige da direbanci don ya samu ya rufawa kansa asiri.
Alh. Abdullah ya xago kan ‘yar tasa yana goge mata hawaye, cikin qunan zuci, ki ci gaba da
wannan halin ba, insha Allahu kina kammala karatu ki zan miki aure kin ji.’
Ta xago tana dubansa “Waye zai ayreta a haka?” Ta ayyana a ranta, “Abba don Allah
tunda mun samu hutu ka bar ni in je gidan yaya Rahma.” Ya xan yi shiru, can ya ce to Asma’u kin
san dai Auntynki ba za ta bar ki ba.”
bar ki ba.”
Wani haushi ta kuma ji sam bata son Abbanta yana gaya mata haka, wato ba shi ke da iko da ni
ba ita ce. Shiru ya yi can ya ce “To ki je ki shirya kayan ki yanzu direba zai dawo sai ya kai ki, amma ba
ni son ki sanar da kowa, don muddin ta sani dole zata hana ki.”
cikin murna ta ce, “Yauwa Abba, na gode.” Ta bar jikin motar ya ce direba zai kawo miki kuxi
sai abin da ki ke so.” Ta ce “Abba na gode, sai munyi waya ta wayar Rahma.”
Muna har ciki, gidan su qawarta ta samu shiga Aisha dama maqotansu ce ta sanar da ita, ta ce, kai ina
miki murna, ko ba komai kya xan huta kafin ki dawo.”

A hanya direba yahaya sai kallonta yake yi da gefen ido, yarinyar tana bala’in bashi tausayi, gagt
kyakkyawa da ita fafra ce tas da ba zai manta da Ummanta ba, kamar su xaya da ita don mahaifiyarsu
sa’adatu Balarabiya ce a saudiya mahaifinta ya aureta.
Sa’adatu kamarta xaya da uwarta, itama Asma’u kamarta xaya da mahaifiyarta, sai dai har tafi
kama da kakarta, fara ce tas mai doguwar fuska da dogon hanci, ga yalwataccen gashin kai. Tsayawa
tsara yanayin Asma’u vata lokaci ne.
Kyakkyawa ce sosai ga kyan diri duk ta haxa shi, sam Yahya bai gajiya da kallon yarinnyar tare
da tausaya mata, can ya katse shirun da cewa.
“Hutun naku da yawa kenan?”Ta ce eh, sati biyar ne. Ya ce “A lallai za ki jima , sai ki daurevki
samoo mana xan zariya tunda kin ji Alhaji ya ce kina yin candy aurar da ke zai yi.”
Murmushi tayi kawai ba ta ce komai ba, ya kuma cewa “ko xan kano za a samo mana?”
Tambayayin sun ishe ta don ita bata fiye son magana ba, ta ce na bar wa Abba na zavi, duk wanda ya
zava min zan aure shi mutuqar zan bar gidan.”
Ya dan sassauta gudu ya ce, Ki daina cewa duk, kar ya samo miki wanda ba ki so.” Tace “zan
zauna da shi koda ba ni sonsa.” Ya xan yi shiiru, “koda yaron gida ne?” Cikin qosawa da tambayoyinsa
ta ce,
“koda Almajiri kan hanya ne, mutuqar ya cika qa’idojin da shari’a ta halarta a ba shi aure.” Shiru
yayi bai kuma magana ba, har suka isa zariya.
Cikin murna ita da yaya Rahma suka rungume juna suna murna har da kukansu, shi dai direba
yana kallon ikon Allah, ya jido kayan ciki motar ya fidda su, ruwa kawai yasha ya juya zuwa kano. Yasan
yau akwai case, donn jin Asma’u bata gidan yau sai an raba Alhaji da Hajiya, don ta riga ta saba a gaban
masu aiki maigadi da direba take cin kwalarsa taci mutuncinsa. Rashin sanar da ita tafiyar Asma’u kuwa
ba qariamin tashin hankali zai gani ba.
Da daddare suna xaki har gun sha xaya suna ta hirarsu ta ‘yan uwa. Asma’u da ke kwance
tsakiyar ‘ya’yan Rahmasu uku da rigar barci a jikinta, ta ce “Aunty kije gun mijinki tun xazu fa yana ta yi
miki filashin.”
Ta miqe, yau ai dole yayi min uzuri don ina tare da ‘yar uwata, kije dai ai san samu ne Abba ya
bar min ke. Ta riqe baki, kema hira ki ke wannan zuwan ma Allah ne kawai yasan yanda zasu yi, kema
kkin sani.
Washegari sun haxu a falo dukkan su suna break fast har da mijin Rahma Auwal, bayan sun ga
ma kayawa ma da ya fita nan suka zube suna ta hirarsu. Rahma tace “Ni kin san wani abu?” Ta ce “A’a”
“Da ana badawa gashinki za ki qara min.”
Ta kai hannu ta shafi kanta, Allah kenan! kin san me? wai duk nafi ‘ya’yanta gashi, shi
ne take sa almakashi tana yanke min. Kin ga wani iko daga Allah kamar qara shi ake yi. Yanzu a haka an

yanke gashin nan? Kwarai kuwa, sau ukku nace miki na ukunne Baba ya dinga masifa ranar har
mamaki ya bani.
Ashe zai iya yi wa Aunty faxa haka? Ni yaya na rarsa me na matar nan, in kin ga sabulun
wankana sai kin min kuka, wani lokaci omo ta ke bani wai in yi wanka dashi inna je toilet sai in zubda in
yi wankana haka.
Yanzu haka ban da yau wallahi na kai sati haka nake yin wankan babu sabulu, a cewarta bata
son ta ga nafi ‘ya’yanta.Rahma ta ce, ‘ya zatai, ta manta mu jikokin Balarabiya ce, haihuwar saudiya. Tushenmu da
komai namu na can, haba shi yasa naga duk kin daushe ba kamar da ba. Matar nan Allah ba zai barta haka
ba, tun a duniya zata ga qarshenta.”
“Nima abin da nake faxi kenan, wallahi yaya na tsaneta, daga ita har ‘yan uwanta.” Rahma ta
ce,”Kar ki ce haka. iyayenta sun da kirki da ‘yan uwanta, ita ce dai haka.” Ta ce, Ni ina ruwana, ni dai
duk ta shafa musu bana son duk wanda ya zama jininta, in kin cire qannena, to Allah dai ya shiryata, ba
amin ba yaya, Allah ka watsar da ita kada ya bata ikon shiryuwa, ya tozartata, ya nuna mata halinta tun a
duniya, ba sai taje can ba, yayi mata abinda tayi min, ya….”
Ta rufe mata baki “Ba a haka, ke dai ki manta addu’ar shirya, shi yafi.” Yaya kenan, ba zan
tava yi mata addu’ar Allah ya shirya ta ba, tunda take neman tozarta ni.
Daren yau suna jima hira da muhammad, Asma’u ta ce “yaushe zaka dawo?” Ya xan yi shiru, na
sani kuna cikin kewar rashina, kuyi haquri saura shekara uku in qarasa kakratun in dawo. Rahma ta
sanar dani duk irin halin da kike ciki, ki ci gaba da haquri ina dawowa za ki dawo hannuna da zama.
Duk kuwa irin rigimar da za ayi ba zan fasa ba, dama inna ce gatanmu tunda yanzu ta
rasu dole mu rungumi qadddara. ke dai ki dage kiyi karatu, Allah yayi miki albarka.” Amin Yaya, sasi ka
dawo. zan amshi lambarka a gurin yaya Rahma, ko ta wayar qawayena ma dinga gaisawa.”
Satinta biyu a garin zariya tayi kyau sosai farinta ya kuma fitowa, dama ita gwana son
kwaliya ce, don dai ba ta samun damar yi ne ba. Yaya Rahmam ta sai mata kayan sawa kusan kala
takwas, masu tsada aka xinka mata. Kayan kwalliya kam ba a magana, duk wanda ya santa adaa in ya
ganta yanzu ba zai gane ta ba.
Yanda ta haxu, samari da dattawan zaria sai kawo mata hari suke yi, wani lokaci har dariya suke
bata, ita a ganinta yarinya ce don duka-duaka shekarunta sha biyar, sai dai a ciki take kasancewar tana da
xan jiki ga kyan dire in kin ganta za ki ce takai sha takwas, duk da ba wai tana da qiba sosai ba.
Jikinta dai xan daidai ita ba mai jiki ba, ba za ki kuma ce mata siririya ba. sau biyu tana waya
da na’ima duk a ‘ya’yan Hajiya Zainab su bakwai jininsu yafi haxuwa da ita, don ko ganin tayi Aunty ta yi
wa Asma’u abu tana kuka tare suke yin kukansu, koda yake ta lura duk ‘ya’yan basa sonabi da take yi ea
Asma’u don dai ba yanda za su yi ne.

watanta xaya saura sati guda su koma makaranta, Abbansu ya kirata ya ce zai turo
Yahaya direba gobe yazo xaukarta, a take ta sanya masa kuka, ya katse ta “Kada muyi haka da ke Asma’u,
gobe fa kina son in bar ki kuma dawowa, ina laifi sati hudu?”
“To Abba, ka bari sai saura kwana biyu mu koma.” Ya ce,” To Asama’u sai jumma’a kenan ko?’
Eh, Abba na gode .” Ta bai wa yaya Rahma waya.
Yau sukuku ta wuni saboda jin za ta dawo cikin uqubar gidansu, Wai mutum da gidansu amma
yana gudunsa. rahma ce ta dinga yi mata nasiha da daddare har da Auwal suka dinga kwantar mata da
hankali.
Washegari suka shiga da ita kasuwa suka yi mata siyayya, tsaraba da duk abin da suka san zata
buqata har da ‘yar qaramar waya Auwal ya sai mata, tayi murna sosai. sai dai tana tsoron idan Auntyn ta
ganta da waya qwacewa zata yi, sai dai tayi kaffa kar ta gani.
Ranar Jumma’a da wuri yahaya yazo, duk an loda mata kayanta a but xin mota, tana falo yaran
sun sata gaba da kuka wai sai sun bita, itama kukan take yi, duk yanda rahma tayi don ganin bata yi kuka
ba, sai da ta sanyata kuka
Auwal tsayawa yayi kallon ikon Allah, ya ma rasa wanda zai lallasa a cikinsu da kyar yaja
hannun Asma’u zuwa mota tana kuka. tunda ta fito idon yahaya yake kanta ya qi dauke idonsa a kanta,
riga da siket ne a jikinta na atamfa, xinkin ya xan kamata ta, akwai ratsin kore a atamfar.
Shi yasa tasa kore xin mayafi, takalmi da jakarta ‘yar mitsitsiyar wayarta tana manne da hannunta.
Tayi masa kyau sosai.
Tun da ya xaukota bata yi magana ba, ban da kukan da take yi sai da tayi shiru, sai da yaga ta
tsagaita ya ce, mutan zariya yau sai kano ko? ta xan yi yake, eh ya ya ‘yan qannena kuwa? Lafiya, sai dai
Aunty naku tayi tafiya.
Wani sanyin daxi taji ya ziyarci zuciyarta, amma dai daxewa zata yi ko? Eh to, ban sani ba. Yau
dai kwanansu biyu da tafiya wai sun je gun wani qaninta dake karatu a can turkey tasan Abdullah ne mai
suna Babanta shi ne wanda Aunty tafi so duk a qannenta yanzu shekarunsa biyu a can, yana karantar
accounting. Alhaji dai ya ce sati xaya zata yi, a ranta tace in dai Aunty sai an ganta tunda ba gudun xacin
ran Abba take yi ba haka Yahaya ya dinga janta da hira ita kuma jin Aunty bata gidan ba qramin daxi taji
ba ta biye masa suka dinga hirarsu har suka isa gida duk qannenta suna harabar gidan kowanne su yana
jiran iso warta har Abbansu.
Suna yin parking suka yi kanta, sai da suka kada ita sannan suka qaraso gurin Abbansu, yahaya
direba ya shigo da tsarabar da ta yo wa yara ta shiga raba musu haka dai suka wuni ana hira cikin
qannenta cikin farin ciki ta dinga raywa a ranta ina ma ace haka take kullum a gidan, da me zai dame ta.
Da daddare suna kwance a xakinsu, yau ta samu darajar kwana bisa gado kafin annoba ta dawo
(Aunty). Na’ima ta ce, kinga yanda ki ka yi kyau kuwa? Tayi murmushi, haka kowa yake faxi har fa Abba
sai da ya ce min nayi kyau, eh wallahi kamar ba ke ba.

Habib ya shigo da waya a hannunsa “Ungo na’ima in ji Abba, momy ce. ta ansa suka gaisa, shi
suka gaisa ashe dama kusan kullum sai ya kira sun gaisa da yaran, dama shi akwai shi da son yara.
Na’ima ta ce, ga yaya Asma’u ta dawo ku gaisa, to bata , ta miqa mata ta qi ansa ba yanda ba ta yi
ba ta qi ansa, doleta ce Uncle ta qi karba, me yasa? Ya tambaya, ban sani ba, ta kuma bata ta kuma miqa
mata ta ce tunda ta nace ba zan karxa ba, ba zan yi maganar na dole ta ce masa ta qi ansa.
Sai ma kwantawa tayi ta rufe idanunta bayan sun yi sallama da Uncle xin ta dube ta yaya Asma’u
ba ki kyauta ba. Uncle ya ce bai ji daxin abin da ki ka yi masa ba, ta buxe idonta ba me nayi masa magana
ce na ce bani son yi da shi, ba shi kenan ba.
Ganin yanda ta hayayyoqo mmata sai taja bakinta tayi shiru itama kwantawa tayi tana faxin, to
sai da safe. Allah ya tashe mu lafiya.
Asma’u ba barci tayi ba, kawai haushin Abdullah kawai take ji, akan me zai ne ce da son sai ya
gaisa da ni ba san cewa duk wani jinin Aunty na tsane shi ba ina kuma neman tsare da su dukkansu shi
yasa ko zuwa za a yi gidan bata bin yaran gidan duk da dai ta tava zuwa, ba wanda ya nuna mata qiyayya
daga qannen har iyayen amma duk da haka bata qara sha’awar zuwa ba.
Abu kamar wasu,washegari ma da ya kirayi Abbansu sai da ya ce a bai wa Asma’u ,amma ta qi
anas qememe.Abu kamar wasa,kullum yakira sai ya ce a bata,duk ma wadda ya nufe ta da wayar a ranar
sai yasha masifa.
Dole suke haqkura,shima daga baya yadaina kira,ko ya kira bai ma cewa a bata,ta ce ka shafawa
kanka lafiya irin annoba kawai,don aunty kam annoba ce a cikin al umma,a cewarta.
Sai da Aunty sati biyu cib a (Turkey) sannan ta dawo, yara da Abbansu suka je taro ta a airport,
ita kaxai akabari a gidan ba wanda ya gayyace ta, kuma ko an ce ma taje ba za ta ba, ta gyaraa gidan tsab
ta jera abincin da tayi mata a dinning table duk wani kayan adonta ta voye tare da wayarta da ko su
Na’ima bata bari sun gani ba, balle a samu mai gaya mata.
Gida ya kacame da murnar dawowar momynsu, ita kam baqin ciki kawai take yi saboda
murnarta, fara’artaa, dariyarta kai da duk wani jin daxinta ya qare, tunda annoba ta dawo . Ai kuwa a
ranar ta soma kuka, don kallo xaya tayi mata yanda yarinya ta haxu, tayi kyau sai da gabanta ya fadi.
Da yamma liqis ta tura aka kira mata ita, ta rufe ta da faxan ba gaira ba dalili har da zagin
mahaifiyarta ita abin da ya sa ta kuka kenan, ta tsani a tava Ummanta. Nan take za ki ga vacin ranta
matuqar ki ka tava kika tava mat Ummanta, in ga wanda zata iya ramawa nan anan take akan Ummanta
zata rama ko kuma su kwashi ‘yan kallo don bata yin komai.
Abun jiya ya dawo yau, don Asma’u dai ta koma gidanta na tsamiya, tukurawa Anty har yaso yafi
na da, don dama da haushinta ta tafi zariya bata sanar da ita ba, wannan karon ma abinci gaba xaya ta
daina bata, sai ta wuni ba ta ci komai ba, sai dai in Na’ima ta sato ta kawo mata.

Domin Karanta cikekken labirin Danna Nan:- Komai Yayi Tsanani

labarin da ya wuceKishi Iri Nawa ne
Labarin na GabaKashi Nawa Kishin Bayi ya Kasu?