Addu’ar Da Mutum Zai Faɗa Idan Wani Al’amari Ya Zo Masa Na Farin Ciki Ko Na Baƙin Ciki

0
45

Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya kasance idan wani al’amari ya zo masa da yake faranta masa rai ya ce:
“Alhamdu lil laahil lazi bi ni’imatihi tatimmus saalihaatu”.
{Godiya ta tabbata ga Allah wanda saboda ni’imarsa ce kyawawan ayyuka suke ciki}.
Idan kuma wani al’amari ya zo masa wanda yake ƙi sai ya ce:-
“Alhamdu lil laahi alaa kulli haalin”.
{Godiya ta tabbata ga Allah a cikin kowane hali}.

Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Salati Ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunnah wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceAddu’a Bayan An Gama Cin Abinci
Labarin na GabaAddu’ar Da Ake Yi Bayan An Yi Sallama Daga Wutiri
Suna na Isa Uba Chamo masanin na'ura mai kwakwalwa da ilimin addini da harshen Hausa da kuma ilimin halaiyar dan adam, kuma nine wanda ya samar da wannan manhajar wikiHausa tare da abokaina domin taimaka hausawa wajen samon ilimin cikin harshen Hausa a sauƙaƙe