Addu’ar Cin Abinci

0
17

Idan mutum zai ci abinci sai ya ce:-
“Bismillaahi”.
{Da sunan Allah}.
Idan ya manta to sai ya ce (yayin da ya tuna) :-
“Bismillaahifii auwalihi wa aakhirihi”.
{Da sunan Allah a farkonsa da ƙarshensa}.
Wanda Allah ya azurta da abinci ya ci, to ya ce:
“Allaahumma baarik lanaa fiihi wa aɗ’imnaa khairan minhu”.
{Ya Allah! Ka sanya mana albarka a cikinsa, kuma ka ciyar da mu wanda ya fi shi alheri}.
Wanda kuma Allah ya azurta shi da madara ya sha, to ya ce:
“Allaahumma baarik lanaa fiihi wa zidnaa minhu”.
{Ya Allah! Ka sanya mana albarka a cikinta, kuma ka ƙara mana ita (madara)}.

Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’a Bayan An Gama Cin Abinci danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna wanda Sheikh Sa’ida Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceAddu’o’in Neman Tsayar Da Ruwan Sama
Labarin na GabaAddu’a A Yayin Da Ake Iska
Suna na Isa Uba Chamo masanin na'ura mai kwakwalwa da ilimin addini da harshen Hausa da kuma ilimin halaiyar dan adam, kuma nine wanda ya samar da wannan manhajar wikiHausa tare da abokaina domin taimaka hausawa wajen samon ilimin cikin harshen Hausa a sauƙaƙe