Addu’a Bayan An Gama Cin Abinci

0
22

“Alhamdu lil laahil lazii aɗ’amanii hazaa wa razaƙaniihi min gairi haulin minnii walaa ƙuwwatin”.
{Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya ciyar da ni wannan (abincin), ya azurta ni da shi, ba tare da wata dabara ko ƙarfi daga gare ni ba}.
“Allamdu lil laahi hamdan kasiiran ɗayyiban mubaarakan fiihi gaira makfiyyi walaa muwadda’in walaa mustagnan anhu Rabbunaa”.
{Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, yabo mai yawa, kyakkyawa, kuma abin sanya albarka a cikinsa, (Allah) wanda ba a ɗauke masa azurta bayinsa, kuma ba a rabuwa da shi (a bar nema daga wurinsa), kuma ba a wadatuwa ga barinsa; shi ne Ubangijinmu}.

Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Baƙo Ga Wanda Ya Gayyace Shi Cin Abinci danna nan.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunnah wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

labarin da ya wuceDaga Cikin Addu’o’in Roƙon Ruwa
Labarin na GabaAddu’ar Da Mutum Zai Faɗa Idan Wani Al’amari Ya Zo Masa Na Farin Ciki Ko Na Baƙin Ciki
Suna na Isa Uba Chamo masanin na'ura mai kwakwalwa da ilimin addini da harshen Hausa da kuma ilimin halaiyar dan adam, kuma nine wanda ya samar da wannan manhajar wikiHausa tare da abokaina domin taimaka hausawa wajen samon ilimin cikin harshen Hausa a sauƙaƙe